Posts

HASASHEN KIMIYYA 8 DA SUKA FARU A ZAHIRI

Image
  Hasashen Kimiyya 8 Da Suka Faru a Zahiri Akwai dubunnai  hasashen kimiyya  da suka faru a rayuwa ta zahiri, waɗanda yawancinsu sun samo asali ne daga ƙirƙirarrun labaran  kimiyya  da marubuta suka yi ta yin hange a kai a matsayin tatsuniya. Amma a yau waɗannan hasashe na ƙirƙirarrun labaran sun tabbata a rayuwa ta zahiri, kaɗan daga cikin waɗanda za a iya sani a wannan rubutun sun haɗa da: 1. Saƙago Da abu ne mai wuya a wayi gari wani yayi tunanin kasantuwar saƙagai a rayuwa ta zahiri, amma a yau sun zama ruwan dare a ko’ina a faɗin duniya. Saƙagai suna taimaka wa mutane a wurare da dama, kuma suna da hatsari a wurare da dama. Haƙiƙa  rayuwar saƙago  da mutane abu ne da ke buƙatar nazari da kula da kuma sanin yadda za a kafa kyakkyawar mu’amala a tsakani. 2. Saƙa-Mutum Saƙa-mutum  shi ne mutumin da aka sabunta ko maye gurbin wasu sassan jikinsa da na saƙago, sannan sai/ko kuma sabunta mutumin sukutum zuwa mataki na gaba. Babu wanda yayi tunanin ...
Image
  Hasashen Kimiyya: Mai Yiwuwa ko Akasinsa? Sau tari mu kan iya cewa kimiyya tana tafiya ne da hasashe, wanda yake taimaka mata domin samun damar binciko wasu abubuwa masu amfani dangane da ita da kuma fadada kirkira a zamanance. Hasashe anan shine tunanin faruwar wani lamari nan gaba wanda ba lalle ba ne ya iya zama gaskiya. Dan haka, tunani akan faruwar wasu lamura na kimiyya sune hasashen kimiyya. Akwai lamura da dama da aka yi hasashen faruwarsu a kimiyya, wadanda yiyuwa ko rashin yiwuwarsu kila-wa-kala ne. A duniyar kimiyya da fasaha akan iya yin hasashen wasu lamura ko da kuwa akan shafe shekaru sama da dari ne ba a gano su ba. Misali, masani Edward Teller ya ce “…ban fitar da rai ba ko da zuwa nan da shekaru 500 ne cewa za a iya samun wani jirgi da zai yi gudu kamar gudun haske.” Kenan wannan hasashe ko fata na masani Teller shi yake karfafawa masana kimiyya gwiwwa domin bincike wajen gano wannan abun. Haka nan ka kan iya hasashen cewa ko da nan da shekaru 50 masu zuwa idan ...

ME ZAKA IYA SANI GAME DA TIME TRAVEL?

Image
Asalin kimiyyar ta fara kasantuwa ne a kagaggun labarai wato sci-fi (science fiction) kamar yadda na fada satin da ya gabata cewa wasu daga cikin fikirori ko nazariyyoyin kimiyya suna fara kasantuwa ne a irin wannan halin da kuma tunani (imagination) wanda ya kasance makasudin ilimi, inji babban masanin kimiyya Albert Einstein. Wato Time Travel a kimiyyance shine tafiya cikin lokaci, ko ko muce kamar rufa ido ne na lokaci (illusion of time), wanda ake tunanin zai iya faruwa a rayuwa ta zahiri. A takaice time travel tafiya ce izuwa sararin samaniya; watakila wasu duniyoyi, gungun taurari, ko kuwa dai kutsawa cikin samaniya domin binciken wasu abubuwa, don mayar da irin wannan tafiya ta zama cewa zamu iya tsallakawa zuwa wani zamani saboda banbancin wuri (space) wanda ya ta’allaka da lokaci (time). Gane wannan nazariyya cikin sauki shine komawa baya domin fahimtar nazariyyar Albert Einstein ta relativity a inda yake nuna cewa lokaci (time) da wuri (space) suna ta’allaka da juna da wurin ...

TRUECALLER TANA NUNA SUNAN KARYA?

Image
Sau tari zaka rika ji mutane suna korafi akan Truecaller idan aka kira lambarsu sai Sunan wani ya fito maimakon nasu. Abin da ciwo ka mallaki layi da kudinka amma sunan da zai bayyana wa mutane ya zama sunan wani. Wasu na iya maka kallon Dan Basaja ko dai mara gaskiya saboda rashin sanin hakikanin yadda Truecaller ke aiki.  Idan Allah Ya nufa ka karanta rubutun da ya gabata mai taken TRUECALLER NA SACE LAMBOBI?  Zaka fahimci yadda Manhajar ke aiki, zai kuma zama matashiya akan wannan rubutun. DALILAN DA YASA TRUECALLER KE NUNA SUNAN KARYA. 1. Idan masu aiki da Truecaller mafi rinjaye suka adana labarka ba daidai ba, a haka Manhajar zata fahimci sunan, ta cigaba da bayyanashi wa mutane. Misali, mu dauka cewa ainihin Sunanka Sani Muhammad, amma sa'anarka Trader ce. Idan abokan huldar kasuwancinka suka adana lambarka da "Sani Mai Trader" to a haka Manhajar Truecaller zata nunawa masu amfani da ita. A irin haka, mun taba cin karo da korafin wani Senior Criminal Lawyer, inda y...

TRUECALLER NA SACE LAMBABOBI?

Image
Yadda Manhajar Truecaller ke aiki. Kana iya tuna a karo na farko, lokacin da ka girke Truecaller a wayarka, yadda kake jin dadi ta hanyar gano lambar mutumin da baka sani ba? Ga wasu mutane, abin yana kama da siddabaru. To amma, ta yaya truecaller ta fara kafuwa har ta samu nasarar gano kusan dukkan sunayen lambobin mutane? Manhajar Truecaller Truecaller ta fara ne a shekara ta 2009 karkashin jagorancin wasu matasa dalibai biyu, Nami Zarringhalam da Alan Mamedi dake wani birni, Stockholm a kasar Sweden. A lokacin da aka sake Truecaller a yanar gizo ya samu nasara mai yawa na saukarwa 10,000 a cikin mako daya. A wancan lokacin, asusun adana bayanai na Truecaller a iyakance yake, saboda haka bai iya gano kowace lamba. Amma a kwana a tashi, yanzu komi ya inganta. A lokacin da akayi wannan rubutu, an sauke Truecaller app sama da miliyan 500+. A Yanzu wannan Manhaja na iya gane yawancin kiran lambobin da ba'a sani ba a Duniya. Ba wai kawai gano sunayen lambobi ba, an kara fadada aikace ...

ABUBUWA 12 DA BAI KAMATA KA WALLAFA A FACEBOOK BA.

Ko da kana tunanin ka saita “Privacy” baka da tabbacin iyakar masu ganin bayanan da kake rubutawa. Baka da ikon kayyade abinda abonkanan ka zasu iya yi da bayanan da kake wallafawa. Kada kayi la’akari da karancin “comments” ko “likes” saboda masu karanta rubutunka suyi gaba sun fi yawa ba tare da ka sani ba. Kenan abu ne mai sauki post dinka ya bayyana a inda baka tsammani musamman idan aka yi “searching”. Ga wasu abubuwa guda goma sha biyu masu muhimmanci da ya kamata ka killace daga Facebook. 1.Bayanai game da kai na hakika wadannan suka shafi sirrinka na zati. Kada ka rubuta abinda ka san ya dace da bayananka na banki irin su; adireshin gida, sunan mahaifiya, lambar waya, kwanan watan haihuwa da dukkan dangogin su. Irin wadannan bayanai ne masu “satar zati” (identity-teft) suke sacewa suna aikata ta’adancin yanar gizo (cyber crime). Saboda haka maganin da banyi ba shine ban fara ba. 2.Kalmomin sirrin ko ta kwana “password hints” da “security questions.” ...

YI KIRA KYAUTA TARE DA CUG SIM CARD

Image
YI KIRA KYAUTA TARE DA CUG SIM CARD. Matashiya; Kaman yadda muka yi alƙawari a baya cewa post na gaba zai yi bayani akan layin POL COM ko CUG, to gashi Allah Ya nufa. A baya mun yi bayani game da SPECIAL NUMBER da alfanun sa, yanzu kuma zamu yi bayani akan CUG SIM wanda ake yin kira kyauta dashi. MENE NE POL COM ko CUG? CUG (Closed User Group) layi ne wanda kamfani take bugawa don jami'an tsaro ko hukumomin gwamnati don saukaka masu wajen yin kira ba tare da sisin kwabo ba. A da can kamfanin GLO NG ne kadai suke buga irin wadannan nau'ikan layika, amma yanzu sauki yazo saboda shahararren kamfanin Airtel Nigeria yayi hobbasa ya fitar da CUG SIM CARD don saukakawa dukkan yan kasa. ALFANUN CUG SIM CARD. 1. Kira kyauta daga CUG zuwa CUG. 2. x10 bonus a kowane lodin da aka yi. Bonus ɗin yana rabuwa kashi kashi kaman haka; a) Bangaren kiran kowane network, b) Bangaren kiran Airtel zuwa Airtel, c) Bangaren kiran Family And Friends (FAF) ma'ana yan uwa da abokan ...

SPECIAL NUMBER DA ALFANUN TA

Image
ALBISHIR DIN KU KANAWA!!! Ga wata dama tana zuwa da ba kasafai ake samun irin ta ba. Shin ko ka taba mallaka ko jin labarin layin waya da ake yiwa lakabi da suna SPECIAL NUMBER? Ka taba mallaka jin labarin wasu layikan waya POL COM da CUG? Shahararren kamfanin na wato Airtel Nigeria ya zo maku amsoshin tambayoyin dake sama. MENE NE SPECIAL NUMBER? Special number layi ne na musamman da ba kasafai ake samun irin sa ba, layi ne da kamfani take bugawa domin saukakawa kwastomomi wajen haddace lambobi. ALFANUN SPECIAL NUMBER 1. Manyan mutane, yan kasuwa, gidajen Radiyo da na Talabijin suna amfani da special numbers don saukaka mu'amala ga abokan hulɗar su. 2. Special number yana da kwarjini da burge mutane a duk lokacin da ake karanta shi. 3. Yana zuwa da wasu damammaki da ba a cika samu a layika gama gari ba. 4. Yana zuwa da fasaha mafi ƙarfi wato wajen kira da saurin shiga yanar gizo wato 4G LTE. 5. Yana zuwa da "double data offer" ma'ana za...

GARABASA

Image
GARABASA Shahararren kamfanin sadarwa na  Airtel Nigeria  ya sake zuwa da wata sabuwar garabasa a bangaren data. Da kudi kalilan zaka sayi data mai dimbin yawa ta yadda zaka samu daman shiga yanar gizo, ka sauke abubuwa masu yawa da kudi kadan. A yanzu dai kamfanin ta ribanya adadin datar da take bayarwa har sau biyu ba tare da ta kara sisin kwabo ba. Wannan ba karamin ci gaba bane musamman ga 'yan makarantar da waɗan da basu da mahaɗar Wi-Fi da masu karamin karfi idan aka yi d uba da yadda al'amuran yau da kullum suke ta komawa yanar gizo. Ga jerin lambbobin sayan datar a kasa: 1.5GB akan ₦500 danna *418# 3GB akan ₦1000 danna *496# Idan kana son sayen datar sama da haka, danna *141# sai ka canki zabin ka. Abin lura: Wannan garabasa tana aiki ne akan sabon layin Airtel. Idan baka da shi kayi maza ka garzaya shagon Airtel mafi kusa da kai saboda kada ayi ba kai. Masu tsofin layin Airtel zasu danna *144# don duba cancanta. Muna maraba da karin b...

MENE NE 4G LTE?

Image
4G LTE Kana son shiga cikin masu more tsarin fasahar internet mafi sauri a wayar ka? Yi maza ka koma kan fasahar 4G LTE . MENE NE 4G LTE? Fourth Generation Long Term Evolution , wanda aka fi sani da 4G LTE shine fasaha mafi sauri wajen gudanar da ayyukan yanar gizo a Nigeria, yana samun karbuwa wajen masu amfani da manyan wayayoyi masu dauke da manhajar komi da ruwanka wato Android , da Mi-Fi ko Router da kuma Modem . 4G LTE fasaha ce mai saurin gaske wadda take bada damar gudanar da ayyuka masu nauyi cikin kyaftawar ido. Zaka iya yin kira mai hoto rangadadau wata " HDvideo call " ba tare da wani jinkiri ba. Zaka iya sauko da lodi mai nauyi cikin kankanin lokaci. Da 4G LTE , zaka iya kallon tafsir kai tsaye ta cikin youtube ko facebook go live, ko live on instagram. KAMFANONIN DA SUKE DA FASAHAR 4G LTE A NIGERIA. 9mobile (Etisalat) a da, Globacom, MTN, NTEL, Spectranet, Swift, Smile, Airtel. Za mu dau misalin yadda ake shiga tsarin fasaha...