Posts

Showing posts from November 25, 2018

ABUBUWA 12 DA BAI KAMATA KA WALLAFA A FACEBOOK BA.

Ko da kana tunanin ka saita “Privacy” baka da tabbacin iyakar masu ganin bayanan da kake rubutawa. Baka da ikon kayyade abinda abonkanan ka zasu iya yi da bayanan da kake wallafawa. Kada kayi la’akari da karancin “comments” ko “likes” saboda masu karanta rubutunka suyi gaba sun fi yawa ba tare da ka sani ba. Kenan abu ne mai sauki post dinka ya bayyana a inda baka tsammani musamman idan aka yi “searching”. Ga wasu abubuwa guda goma sha biyu masu muhimmanci da ya kamata ka killace daga Facebook. 1.Bayanai game da kai na hakika wadannan suka shafi sirrinka na zati. Kada ka rubuta abinda ka san ya dace da bayananka na banki irin su; adireshin gida, sunan mahaifiya, lambar waya, kwanan watan haihuwa da dukkan dangogin su. Irin wadannan bayanai ne masu “satar zati” (identity-teft) suke sacewa suna aikata ta’adancin yanar gizo (cyber crime). Saboda haka maganin da banyi ba shine ban fara ba. 2.Kalmomin sirrin ko ta kwana “password hints” da “security questions.”