Posts

Showing posts from May 13, 2018

MENE NE 4G LTE?

Image
4G LTE Kana son shiga cikin masu more tsarin fasahar internet mafi sauri a wayar ka? Yi maza ka koma kan fasahar 4G LTE . MENE NE 4G LTE? Fourth Generation Long Term Evolution , wanda aka fi sani da 4G LTE shine fasaha mafi sauri wajen gudanar da ayyukan yanar gizo a Nigeria, yana samun karbuwa wajen masu amfani da manyan wayayoyi masu dauke da manhajar komi da ruwanka wato Android , da Mi-Fi ko Router da kuma Modem . 4G LTE fasaha ce mai saurin gaske wadda take bada damar gudanar da ayyuka masu nauyi cikin kyaftawar ido. Zaka iya yin kira mai hoto rangadadau wata " HDvideo call " ba tare da wani jinkiri ba. Zaka iya sauko da lodi mai nauyi cikin kankanin lokaci. Da 4G LTE , zaka iya kallon tafsir kai tsaye ta cikin youtube ko facebook go live, ko live on instagram. KAMFANONIN DA SUKE DA FASAHAR 4G LTE A NIGERIA. 9mobile (Etisalat) a da, Globacom, MTN, NTEL, Spectranet, Swift, Smile, Airtel. Za mu dau misalin yadda ake shiga tsarin fasaha