ABUBUWA 12 DA BAI KAMATA KA WALLAFA A FACEBOOK BA.

Ko da kana tunanin ka saita “Privacy” baka da tabbacin iyakar masu ganin bayanan da kake rubutawa. Baka da ikon kayyade abinda abonkanan ka zasu iya yi da bayanan da kake wallafawa. Kada kayi la’akari da karancin “comments” ko “likes” saboda masu karanta rubutunka suyi gaba sun fi yawa ba tare da ka sani ba. Kenan abu ne mai sauki post dinka ya bayyana a inda baka tsammani musamman idan aka yi “searching”. Ga wasu abubuwa guda goma sha biyu masu muhimmanci da ya kamata ka killace daga Facebook.
1.Bayanai game da kai na hakika wadannan suka shafi sirrinka na zati. Kada ka rubuta abinda ka san ya dace da bayananka na banki irin su; adireshin gida, sunan mahaifiya, lambar waya, kwanan watan haihuwa da dukkan dangogin su. Irin wadannan bayanai ne masu “satar zati” (identity-teft) suke sacewa suna aikata ta’adancin yanar gizo (cyber crime). Saboda haka maganin da banyi ba shine ban fara ba.
2.Kalmomin sirrin ko ta kwana “password hints” da “security questions.” Kada ka fitar da kalmomin sirri na “ko ta kwana” da ake tambaya yayin rijistar akawun irin su; kwanan watan haihuwa, abincin da kafi so, garin da ka girma, abokinka na yarinta da sauransu. Da irin wadannan bayanan hacker zai iya yin kirdado ya shigar da bayanan ta hanyar kwarewa ya kwace maka ragamar ikon akawun.
3.Boye inda ka fito, inda kake da kuma inda zaka je. Idan ba ya zama dole ba, kada ka bayyana wuraren da kake yawan ziyarta saboda halin yau. Ba daidai ba ne ka rika fadawa duniya cewa zaka je hutun karshen mako waje kaza, babu laifi don ka roki abokai su tayaka da addu’a akan balaguron da zaka yi, amma kuskure ka bayyana lokaci da inda zaka je. Mu daure mu rika gujewa wasu abubuwan saboda tsaro ba don tsoro ba.
4.Banda yawan fahariya. Kada ka zama mai yawan cika baki a cikin rubutunka, ka kasance mai kakan da kai, duk wanda yace shine wane to ba shi ba ne. Yawan fahariya yana rage daraja a idon abokai.
5.Kada ka rika rubuta abinda zai ja hankalin jama’a da gangan masali, ka fara yin rubutu a kan wani abu mai tada hankali kuma ka ki karasawa kawai don ka tursasa mai karatu ya tambaye ka abunda yake faruwa.
6.Kada ka rika bayyana abinda ya shafi rayuwarka na sirri. Ba ayi ciki don cin abinci kadai ba, ka sirrinta duk wasu al’amuran da suka shafi rayuwarka na sirri. Babu laifi don ka bayyana wani abu na farin ciki a tare da kai, amma kayi tunani kafin ka rubuta.
7.Kada ka dora hotunan aibu akan abokinka don ayi dariya, wani zai iya saukewa ya sake sarrafa su ta hanyar da bata dace ba.
8.Kada ka rika dora hotunan yara da sunayensu a facebook, idan ma hakan ya zama dole to ka nemi izini daga iyayensu. Hotunan yara yana da hatsari a yanar gizo, Allah Ya tsare!
9.Kada ka aika hotunan sirri ta message. Mutane da yawa idan sun tura hutunan sirri ta messanger suna zaton babu wani mahalukin da zai iya gani sai wanda aka turawa, idan kana cikinsu to daga yau ka fita. Duk hoton da kasan baka son duniya ta gani to kada ka aika shi ta messanger.
10. Banda yawan korafi akan aikin ka. Yawan korafi game da aikin da kake yi zai iya haifar maka da wata matsala da ma’aikatarka ko maigidanka. Kuma zaka ragewa kanka kima a idanun mutane da yawa, saboda zasu rika yi maka kallon wanda bashi da sirri kuma mara godiya da abunda ya samu.
11. Siyasa!!! A cikin 'yan shekarun nan, rikice-rikice na siyasa a kan Facebook ya karu sosai. Mutum daya ne tak zai bayyana ra’ayinsa, amma zaka ga daruruwan mutane mabambanta ra'ayoyi sun yo caaa suna ta jayayya. Akwai mutanen da suka rasa abokai akan Facebook saboda bambancin ra’ayi na siyasa. Duk lokacin da zaka wallafa wani abu game da siyasa, ka tsaya kayi nazari kuma kayi rubutu bisa adalci da gaskiya, idan kayi haka tamkar ka kare mutumci ka ne sannan duk wanda bai mutumta ra’ayinka a wannan mataki ba, to bai cancaci ya zama abonkin ka ba.
12. Labaran bogi ko wadanda ba’a tantance ba. Labaran boki yanzu sun zama ruwan dare, kana wallafa labari zai kama yaduwa kaman wutar daji. Saboda haka, kafin ka wallafa labari a yanar gizo, ka tabbatar ka tantance shi, kuma sahihi ne mai tushe. Duk da haka, kada ka yada labarin da ka san zai iya tada zaune tsaye. Mu guji yada labaran da suka shafi cin zarafin mutum, al'ada, addini da sauransu. Rubutu idan kayi shi baka san iyakar inda zai kai ba, Rubutu shi yake kulla alakar fahimta tsakanin mai wallafawa da mai karantawa, saboda haka mu rika amfani da rariyar tunani don tankade abinda zuciya zata sa hannaye su rubuta.
Allah Ya taimaki kasar mu Nijeriya, Ya zaunar da ita lafiya, Ya kare ta daga sharrin masu sharri.

Ziyarci shafin mu na facebook Duniyar Yana don samun sabbin bayanai.

Comments

Popular posts from this blog

GARABASA

MENE NE 4G LTE?

HASASHEN KIMIYYA 8 DA SUKA FARU A ZAHIRI