TRUECALLER TANA NUNA SUNAN KARYA?

Sau tari zaka rika ji mutane suna korafi akan Truecaller idan aka kira lambarsu sai Sunan wani ya fito maimakon nasu. Abin da ciwo ka mallaki layi da kudinka amma sunan da zai bayyana wa mutane ya zama sunan wani. Wasu na iya maka kallon Dan Basaja ko dai mara gaskiya saboda rashin sanin hakikanin yadda Truecaller ke aiki. 

Idan Allah Ya nufa ka karanta rubutun da ya gabata mai taken TRUECALLER NA SACE LAMBOBI? Zaka fahimci yadda Manhajar ke aiki, zai kuma zama matashiya akan wannan rubutun.




DALILAN DA YASA TRUECALLER KE NUNA SUNAN KARYA.

1. Idan masu aiki da Truecaller mafi rinjaye suka adana labarka ba daidai ba, a haka Manhajar zata fahimci sunan, ta cigaba da bayyanashi wa mutane. Misali, mu dauka cewa ainihin Sunanka Sani Muhammad, amma sa'anarka Trader ce. Idan abokan huldar kasuwancinka suka adana lambarka da "Sani Mai Trader" to a haka Manhajar Truecaller zata nunawa masu amfani da ita.

A irin haka, mun taba cin karo da korafin wani Senior Criminal Lawyer, inda yake cewa Truecaller tana nuna sunanshi da "Senior Criminal." 😃 Hakika dole hankalin wannan lauya ya tashi. Sai da yabi wasu hanyoyin da suka dace ya gyara.


2. Sayen sabon layi; Galibi idan ka sayi sabon layi a kasuwa,  Truecaller na iya nuna sunan wani, ko da kuwa kayi masa rijista da sunanka a wurin da ka sayi layin. Nasha jin korafe korafe daga wajen wadan da suka sayi sabon layi suna tuhumar mai sayar da layi cewa yayi masu rijista da sunan wani, wanda abin ba haka yake ba. Kamfanin Truecaller bata da hurumin shiga kamfanonin sadarwa na masu samar da layika irin su; MTN, Airtel, Glo, 9mobile. Abinda yake faruwa shine, idan ka sayi sabon layi  kuma akayi maka rijista da sunanka, ka dorashi akan waya sai Truecaller ta nuna maka sunan wani, to akwai yiwuwar dama can tsohon layi ne da wani ya taba aiki da shi.


Kamfanonin sadarwa masu samar da layika suna da wasu sharudda da suke gindayawa, daga ciki akwai, idan aka daina amfani da layi har na tsawon wata uku, doka ta basu damar sake buga shi su sayar a kasuwa. Idan kaci karo da irin wadannan layika, bayanan tsohon wanda yayi aiki da layin ne zasu ci gaba da bayyana a Truecaller ko da kuwa anyi maka rijista da sunanka a wajen da ka sayi layin. Ita manhajar Truecaller ba zata iya shiga rumbun adana bayanai na kamfanin sadarwar MTN ko Airtel ta gane cewa an samu canjin mamallakin layin ba, sai dai kai da ka sayi layin ka ziyarci shafin Truecaller don aiwatar da gyara.

Comments

Popular posts from this blog

MENE NE 4G LTE?

TRUECALLER NA SACE LAMBABOBI?

GARABASA

SPECIAL NUMBER DA ALFANUN TA