Posts

Showing posts from 2021

HASASHEN KIMIYYA 8 DA SUKA FARU A ZAHIRI

Image
  Hasashen Kimiyya 8 Da Suka Faru a Zahiri Akwai dubunnai  hasashen kimiyya  da suka faru a rayuwa ta zahiri, waɗanda yawancinsu sun samo asali ne daga ƙirƙirarrun labaran  kimiyya  da marubuta suka yi ta yin hange a kai a matsayin tatsuniya. Amma a yau waɗannan hasashe na ƙirƙirarrun labaran sun tabbata a rayuwa ta zahiri, kaɗan daga cikin waɗanda za a iya sani a wannan rubutun sun haɗa da: 1. Saƙago Da abu ne mai wuya a wayi gari wani yayi tunanin kasantuwar saƙagai a rayuwa ta zahiri, amma a yau sun zama ruwan dare a ko’ina a faɗin duniya. Saƙagai suna taimaka wa mutane a wurare da dama, kuma suna da hatsari a wurare da dama. Haƙiƙa  rayuwar saƙago  da mutane abu ne da ke buƙatar nazari da kula da kuma sanin yadda za a kafa kyakkyawar mu’amala a tsakani. 2. Saƙa-Mutum Saƙa-mutum  shi ne mutumin da aka sabunta ko maye gurbin wasu sassan jikinsa da na saƙago, sannan sai/ko kuma sabunta mutumin sukutum zuwa mataki na gaba. Babu wanda yayi tunanin za a iya yin wannan a zamanin da ya wuc
Image
  Hasashen Kimiyya: Mai Yiwuwa ko Akasinsa? Sau tari mu kan iya cewa kimiyya tana tafiya ne da hasashe, wanda yake taimaka mata domin samun damar binciko wasu abubuwa masu amfani dangane da ita da kuma fadada kirkira a zamanance. Hasashe anan shine tunanin faruwar wani lamari nan gaba wanda ba lalle ba ne ya iya zama gaskiya. Dan haka, tunani akan faruwar wasu lamura na kimiyya sune hasashen kimiyya. Akwai lamura da dama da aka yi hasashen faruwarsu a kimiyya, wadanda yiyuwa ko rashin yiwuwarsu kila-wa-kala ne. A duniyar kimiyya da fasaha akan iya yin hasashen wasu lamura ko da kuwa akan shafe shekaru sama da dari ne ba a gano su ba. Misali, masani Edward Teller ya ce “…ban fitar da rai ba ko da zuwa nan da shekaru 500 ne cewa za a iya samun wani jirgi da zai yi gudu kamar gudun haske.” Kenan wannan hasashe ko fata na masani Teller shi yake karfafawa masana kimiyya gwiwwa domin bincike wajen gano wannan abun. Haka nan ka kan iya hasashen cewa ko da nan da shekaru 50 masu zuwa idan aka

ME ZAKA IYA SANI GAME DA TIME TRAVEL?

Image
Asalin kimiyyar ta fara kasantuwa ne a kagaggun labarai wato sci-fi (science fiction) kamar yadda na fada satin da ya gabata cewa wasu daga cikin fikirori ko nazariyyoyin kimiyya suna fara kasantuwa ne a irin wannan halin da kuma tunani (imagination) wanda ya kasance makasudin ilimi, inji babban masanin kimiyya Albert Einstein. Wato Time Travel a kimiyyance shine tafiya cikin lokaci, ko ko muce kamar rufa ido ne na lokaci (illusion of time), wanda ake tunanin zai iya faruwa a rayuwa ta zahiri. A takaice time travel tafiya ce izuwa sararin samaniya; watakila wasu duniyoyi, gungun taurari, ko kuwa dai kutsawa cikin samaniya domin binciken wasu abubuwa, don mayar da irin wannan tafiya ta zama cewa zamu iya tsallakawa zuwa wani zamani saboda banbancin wuri (space) wanda ya ta’allaka da lokaci (time). Gane wannan nazariyya cikin sauki shine komawa baya domin fahimtar nazariyyar Albert Einstein ta relativity a inda yake nuna cewa lokaci (time) da wuri (space) suna ta’allaka da juna da wurin