Posts

Showing posts from September 13, 2020

TRUECALLER TANA NUNA SUNAN KARYA?

Image
Sau tari zaka rika ji mutane suna korafi akan Truecaller idan aka kira lambarsu sai Sunan wani ya fito maimakon nasu. Abin da ciwo ka mallaki layi da kudinka amma sunan da zai bayyana wa mutane ya zama sunan wani. Wasu na iya maka kallon Dan Basaja ko dai mara gaskiya saboda rashin sanin hakikanin yadda Truecaller ke aiki.  Idan Allah Ya nufa ka karanta rubutun da ya gabata mai taken TRUECALLER NA SACE LAMBOBI?  Zaka fahimci yadda Manhajar ke aiki, zai kuma zama matashiya akan wannan rubutun. DALILAN DA YASA TRUECALLER KE NUNA SUNAN KARYA. 1. Idan masu aiki da Truecaller mafi rinjaye suka adana labarka ba daidai ba, a haka Manhajar zata fahimci sunan, ta cigaba da bayyanashi wa mutane. Misali, mu dauka cewa ainihin Sunanka Sani Muhammad, amma sa'anarka Trader ce. Idan abokan huldar kasuwancinka suka adana lambarka da "Sani Mai Trader" to a haka Manhajar Truecaller zata nunawa masu amfani da ita. A irin haka, mun taba cin karo da korafin wani Senior Criminal Lawyer, inda y