Posts

Showing posts from September 6, 2020

TRUECALLER NA SACE LAMBABOBI?

Image
Yadda Manhajar Truecaller ke aiki. Kana iya tuna a karo na farko, lokacin da ka girke Truecaller a wayarka, yadda kake jin dadi ta hanyar gano lambar mutumin da baka sani ba? Ga wasu mutane, abin yana kama da siddabaru. To amma, ta yaya truecaller ta fara kafuwa har ta samu nasarar gano kusan dukkan sunayen lambobin mutane? Manhajar Truecaller Truecaller ta fara ne a shekara ta 2009 karkashin jagorancin wasu matasa dalibai biyu, Nami Zarringhalam da Alan Mamedi dake wani birni, Stockholm a kasar Sweden. A lokacin da aka sake Truecaller a yanar gizo ya samu nasara mai yawa na saukarwa 10,000 a cikin mako daya. A wancan lokacin, asusun adana bayanai na Truecaller a iyakance yake, saboda haka bai iya gano kowace lamba. Amma a kwana a tashi, yanzu komi ya inganta. A lokacin da akayi wannan rubutu, an sauke Truecaller app sama da miliyan 500+. A Yanzu wannan Manhaja na iya gane yawancin kiran lambobin da ba'a sani ba a Duniya. Ba wai kawai gano sunayen lambobi ba, an kara fadada aikace