Hasashen Kimiyya: Mai Yiwuwa ko Akasinsa?

Sau tari mu kan iya cewa kimiyya tana tafiya ne da hasashe, wanda yake taimaka mata domin samun damar binciko wasu abubuwa masu amfani dangane da ita da kuma fadada kirkira a zamanance.

Hasashe anan shine tunanin faruwar wani lamari nan gaba wanda ba lalle ba ne ya iya zama gaskiya. Dan haka, tunani akan faruwar wasu lamura na kimiyya sune hasashen kimiyya. Akwai lamura da dama da aka yi hasashen faruwarsu a kimiyya, wadanda yiyuwa ko rashin yiwuwarsu kila-wa-kala ne.

A duniyar kimiyya da fasaha akan iya yin hasashen wasu lamura ko da kuwa akan shafe shekaru sama da dari ne ba a gano su ba. Misali, masani Edward Teller ya ce “…ban fitar da rai ba ko da zuwa nan da shekaru 500 ne cewa za a iya samun wani jirgi da zai yi gudu kamar gudun haske.”

Kenan wannan hasashe ko fata na masani Teller shi yake karfafawa masana kimiyya gwiwwa domin bincike wajen gano wannan abun. Haka nan ka kan iya hasashen cewa ko da nan da shekaru 50 masu zuwa idan aka samu maganin cutar daji (cancer) to za ka yi farin ciki da hakan, ko kuma ka ce burinka shine gano wannan maganin cutar.

Daga cikin abubuwan da aka yi hasashen faruwarsu wadanda duniya take shakkar faruwarsu sun hada da:

#1. Time travel

Time Travel a kimiyyance shine tsallaka wani zamani ba tare da ganinsa ba wanda ake tunanin zai iya faruwa a rayuwa ta zahiri. Wannan hasashen kimiyya yana kokarin ba wa mutum damar yin wata tafiya domin tsallake wani lokaci da zai faru a nan gaba. Misali da ace mutum ya san annobar Covid-19 za ta faru a shekarar 2020, to da kuwa tuni ya tsallake shekarar nan a jerin shekaru wato ba zai ga abunda zai faru a wannan shekarar ba. Wannan hasashe ya rabu kashi biyu: na farko tsallake wani zamani na gaba, na biyu kuma tafiya domin komawa baya. Wannan na biyun yana nuna cewa mutum zai koma shekarun baya yayi rayuwa da kakannin kakanninsa.

#2. Technological singularity

Wato wannan wani hasashe ne na kimiyya hade da fasaha wanda yake fatan adana bayanan da suke kwakwalwar Dan-Adam, ta yadda ko bayan ya mutu za a iya amfani da bayanan nan a cikin na’ura. Watakila a iya amfani da bayanan nan a kwakwalwar sakago, wato sai a tada mutum ya zama cewa kamar dama bai mutu ba.

A cikin wani rubuta na “Menene Asalin Mission na Boca” na kawo bayani kan yadda hasashen fasaha ya tafi cewa za a iya dawo da mutum bayan ya mutu. Wannan kudiri na fasaha da kimiyya akan dawo da mamaci hakika ya ja hankalin masana da dama a duniya musamman wadanda ba su taba tunanin yiwuwar abun ba.

Manyan masana a wannan bangare sun hada da Ray Kurzweil mawallafin littafin The Singularity is Near, Peter Norvig mawallafin littafin AI: The Modern Approach, da kuma su Andrew Ng da sauransu. Wadannan masana suka ce matukar aka fadada bincike to shekarar 2045 za ta iya zama shekarar da za a fara amfani da wannan hasashe na fasaha, amma daga baya kuma Ray Kurzweil ya ce shekarun sun yi kadan sai dai a kara wasu.

#3. Transhumanism

Wannan hasashe na kimiyya da fasaha yana kokarin sabunta mutum ne zuwa mataki na biyu (2.0) ta yadda mutum zai iya yin wasu abubuwan da ba a iyawa da, sannan zai kara kuzarinsa da karfin fikirarsa da sauransu ta hanyar amfani da na’ura da fasahohin zamani. Karfin kuzarin mutum zai karu, zai iya yin wasu abubuwa kamar tashi sama da sauran wasu abubuwan da na’ura take iya yi. Wato dai hada karfi da karfe – hada na’ura da mutum domin zama karfi biyu. A yanzu haka wani kamfani mai suna Neuralink na kasar Amurka yana kokarin hade kwakwalwar mutum ne da na’ura ta yadda duk wani abunda mutum zai iya tunaninsa to za a iya ganinshi a cikin na’ura.

#4. Teleportation

Wannan hasashe na kimiyya yana kokarin cimma kudirinsa ne wajen kawo wani fasali ta yadda mutum zai iya bacewa daga wani wuri ya isa wani wuri ba tare da amfani da abubuwan tafiya na zamani ba, ba kuma tare da amfani da kafarsa ba, kawai dai ya bace daga wani wuri ya isa inda yake so a fadin duniya.

Hakika wannan hasashe na kimiyya ya girgiza mutane a inda suka dauka abun kawai kamar almara ne, wato ba zai taba zama gaskiya ba. Masana suka ce watakila hasashen ya iya zama gaskiya saboda la’akari da nazariyyar “quantum entanglement” wacce Albert Einstein ya kira da “spooky action at a distance”; wato duk suna nufin faruwar wani al’amari a fadin kaunu yana ta’allaka ne da faruwar wani al’amari makamancinsa a wani wuri.

Sannan ana so a yi amfani da kimiyyar “quantum mechanics” ne wajen cimma wannan hasashe ta yadda mutum zai iya bacewa a cikin lokaci kuma ya dawo a cikin lokaci.

#5. Life on other planets

Lokacin da Dan-Adam ya fahimci wannan ce duniyar da yake rayuwa kuma binciken kimiyya ya nuna yiwuwar samun wasu halittu da suke rayuwa a wata duniya musamman a tsarin hasken ranarmu, sai masana suka kudiri bincike kan yadda mutum zai iya yin rayuwa a wata duniya. Rayuwar da mutum zai yi a wata duniya ita ce za ta taimaka wajen ci gaba da fadada bincike a sararin samaniya, bugu da kari kuma za ta iya kawo sauyi a rayuwar wannan duniya saboda rage yawan mutane da za a yi.

Masana suka ce tabbas akwai hikima ta musamman da yasa muke rayuwa a wannan duniya ta earth wacce ita kadai ce batada wani nakasu a dukkanin duniyoyin da suke tsarin hasken ranarmu. Shin tashi daga wannan duniya a koma wata duniyar a ci gaba da rayuwa abu ne mai yiwuwa ko akasin haka musamman idan ka yi duba da wasu barazanar da za a iya fuskanta a can? Masani Elon Musk ya ce yana daga cikin burinsa shine taimakawa wajen mayar da duniyar Mars wacce za a iya rayuwa a cikinta zuwa nan gaba.

Shin a tunaninka wanne ne daga cikin wadannan hasashen kimiyya da fasaha zai iya faruwa?


- Muhammad Auwal Ahmad.

Comments

Popular posts from this blog

MENE NE 4G LTE?

TRUECALLER NA SACE LAMBABOBI?

GARABASA

SPECIAL NUMBER DA ALFANUN TA