YI KIRA KYAUTA TARE DA CUG SIM CARD

YI KIRA KYAUTA TARE DA CUG SIM CARD.

Matashiya; Kaman yadda muka yi alƙawari a baya cewa post na gaba zai yi bayani akan layin POL COM ko CUG, to gashi Allah Ya nufa. A baya mun yi bayani game da SPECIAL NUMBER da alfanun sa, yanzu kuma zamu yi bayani akan CUG SIM wanda ake yin kira kyauta dashi.

MENE NE POL COM ko CUG?

CUG (Closed User Group) layi ne wanda kamfani take bugawa don jami'an tsaro ko hukumomin gwamnati don saukaka masu wajen yin kira ba tare da sisin kwabo ba. A da can kamfanin GLO NG ne kadai suke buga irin wadannan nau'ikan layika, amma yanzu sauki yazo saboda shahararren kamfanin Airtel Nigeria yayi hobbasa ya fitar da CUG SIM CARD don saukakawa dukkan yan kasa.

ALFANUN CUG SIM CARD.

1. Kira kyauta daga CUG zuwa CUG.

2. x10 bonus a kowane lodin da aka yi. Bonus ɗin yana rabuwa kashi kashi kaman haka;

a) Bangaren kiran kowane network,
b) Bangaren kiran Airtel zuwa Airtel,
c) Bangaren kiran Family And Friends (FAF) ma'ana yan uwa da abokan arziki.
d) Kyautar ƙunshin data don shiga yanar gizo.
f) SMS.

3. Ƙirƙirar fasahar 4G LTE tare da Kyautar data har 4GB idan yanki da na'ura duk sun kasance 4G ne.

4. Babu fargaban karewar kudi.

5. Farashi mai rahusa.

KARIN BAYANI

Ana yin kira kyauta ne daga CUG zuwa CUG, Za'a bukaci kwastoma ya loda N700 a kowane wata don shiga kungiyar CUG. Za'a caji kwastoma kudin kira daidai da kowa ga layin da ake kira wanda ba CUG ba.

Muna maraba da tambaya ko karin bayani.

Kada ku manta wannan dama ta fara ne daga yau Litinin 20/8/2018 kuma zata kare ranar Juma'a 24/8/2018 a babban birnin Kano Nigeria.

Ga duk mai bukata,
Hanyar tuntubar mu;
Kira:- 09077744401
WhatsApp:- 08031118845.
Facebook: Duniyar Yana Facebook
Like, Comment, Share.
#AnFara #Kanawa #BarkaDaSallah #POLCOM #CUG #InaCiki #AnaTare

Comments

Popular posts from this blog

GARABASA

MENE NE 4G LTE?

HASASHEN KIMIYYA 8 DA SUKA FARU A ZAHIRI