TRUECALLER NA SACE LAMBABOBI?

Yadda Manhajar Truecaller ke aiki.

Kana iya tuna a karo na farko, lokacin da ka girke Truecaller a wayarka, yadda kake jin dadi ta hanyar gano lambar mutumin da baka sani ba? Ga wasu mutane, abin yana kama da siddabaru. To amma, ta yaya truecaller ta fara kafuwa har ta samu nasarar gano kusan dukkan sunayen lambobin mutane?


Manhajar Truecaller


Truecaller ta fara ne a shekara ta 2009 karkashin jagorancin wasu matasa dalibai biyu, Nami Zarringhalam da Alan Mamedi dake wani birni, Stockholm a kasar Sweden.



A lokacin da aka sake Truecaller a yanar gizo ya samu nasara mai yawa na saukarwa 10,000 a cikin mako daya. A wancan lokacin, asusun adana bayanai na Truecaller a iyakance yake, saboda haka bai iya gano kowace lamba. Amma a kwana a tashi, yanzu komi ya inganta.


A lokacin da akayi wannan rubutu, an sauke Truecaller app sama da miliyan 500+. A Yanzu wannan Manhaja na iya gane yawancin kiran lambobin da ba'a sani ba a Duniya. Ba wai kawai gano sunayen lambobi ba, an kara fadada aikace aikacen Truecaller kaman su, dakatar da kira ko gajeren sako na bogi, tura sakonni kyauta, sakon murya, hada hadar kudade ds.


TA YAYA TRUECALLER KE GANO SUNAYEN LAMBOBI?


Truecaller App ya dogara ne akan tubalin "Crowd Sourcing." Crowd Sourcing wani tsari ne na tattara bayanai daban daban daga ainihin tushen masu amfani da na'ura sannan a kuma yin amfani da su a wasu hanyoyin da suka dace.


Lokacin da wani ya girke manhajar Truecaller a kan wayar sa, manhajar zata nade dukkan sunaye da lambobin na'ura ya taskance a rumbun adana bayanai na Truecaller App. Haka yana nufin idan mutane miliyan 100 ne suka girke Truecaller a cikin wayoyin salula, Manhajar zata nade dukkan sunaye da lambobin wayoyin su. Bayan samun bayanai da dama da suka dace da lissafin algorithm, sai kamfanin ta wallafa wadannan bayanai saboda samuwa ga dukkan masu amfani da Truecaller.


SHIN TRUECALLER NA SACE LAMBABOBI?


Wasu mutane suna tunanin cewa Truecaller na satar lambobin su ba tare da neman wani izni ba. Amma abin ba haka yake ba.


Idan muka duba, dukkan tsarin manhajar ya dogara ne akan bayarwa da karba. Mai amfani da ke son bayani daga lambar da bai sani ba, dole ne ya saukar da lambobinsa zuwa Truecaller. Wato kaman bani gishiri in baka manda kenan. Lokacin da ka girke Truecaller, manhajar zata tambayeka izinin nade lambobi da sunayen wayarka. Idan kace "allow" zatayi "synchronizing" ta dora su a rumbun adana bayanai na kamfanin.


Ba zaka iya aiki da Truecaller ba har sai ka yarda da sharuddansu, dole ka shiga ta hanyar amfani da asusunka na Google ko Hotmail ko facebook don basu daman sarrafa lambobinka.


Ziyarci shafin mu na Facebook DUNIYAR YANA domin samun sabbin rubuce rubucen mu.

Comments

Popular posts from this blog

MENE NE 4G LTE?

GARABASA

SPECIAL NUMBER DA ALFANUN TA