MENE NE 4G LTE?

4G LTE
Kana son shiga cikin masu more tsarin fasahar internet mafi sauri a wayar ka? Yi maza ka koma kan fasahar 4G LTE.

MENE NE 4G LTE?

Fourth Generation Long Term Evolution, wanda aka fi sani da 4G LTE shine fasaha mafi sauri wajen gudanar da ayyukan yanar gizo a Nigeria, yana samun karbuwa wajen masu amfani da manyan wayayoyi masu dauke da manhajar komi da ruwanka wato Android, da Mi-Fi ko Router da kuma Modem.
4G LTE fasaha ce mai saurin gaske wadda take bada damar gudanar da ayyuka masu nauyi cikin kyaftawar ido. Zaka iya yin kira mai hoto rangadadau wata "HDvideo call" ba tare da wani jinkiri ba. Zaka iya sauko da lodi mai nauyi cikin kankanin lokaci. Da 4G LTE, zaka iya kallon tafsir kai tsaye ta cikin youtube ko facebook go live, ko live on instagram.

KAMFANONIN DA SUKE DA FASAHAR 4G LTE A NIGERIA.
9mobile (Etisalat) a da,
Globacom,
MTN,
NTEL,
Spectranet,
Swift,
Smile,
Airtel.

Za mu dau misalin yadda ake shiga tsarin fasahar 4G LTE da kamfanin sadarwa na Airtel Nigeria.
Idan kana da waya mai dauke da fasahar 4G LTE kuma kana da layin Airtel a ciki amma tana nuna maka 3G, to akwai matakai da zaka bi a kasa.
1. Don canjawa daga 3G zuwa 4G akan yawancin Androids, zaka shiga Settings> More> Cellular Network> Preferred Network Type> 4G/3G/2G(auto)
2. Idan ka shigar da ita kan wannan saiti kaga bata nuna 4G ba, to akwai bukatar ka sayi sabon layin 4G a shagon Airtel mafi kusa da kai.
3. Idan baka son canja layi kuma sai ka yi SIM SWAP (Welcome back).
4. Idan ka yi abubuwan da muka lissafa a sama kuma baka ga 4G ba, to lallai babu 4G service a garin da kake. Idan kuma akwai 4G a garin da kake kuma ka bi dukkan matakan sama amma baka ga 4G ba, to ka ziyarci masana harkar waya da kwamfuta mafi kusa da ksi don karin bayani.
A lokacin da muka yi wannan pos din, Airtel 4G yana samuwa ne a wasu birane cikin Nigeriya kamar haka;
IBADAN
LEGAS
OGUN
HABUJA.

A sauran birane Airtel suna samar da network mai ƙarfin 3.75G, mai yiwuwa wannan shine dalilin da ya sa suka dade basu kaddamar da 4G LTE din su ba.
Airtel 4G tana kan kungiya mai lamba 3, mai cin nisan zangon firekanshi 1800MHz, wannan shine ya basu damar yin zarra akan wayoyi da dama irin su tecno, infinix, gionee, itel, nokia and xiaomi wadanda wani lokaci suke bijirewa kamfanonin sadarwa saboda wasu dalilai na kimiyya.

A yanzu haka, Airtel 4G suna da network mai saurin saukarwa 28.45 Mbps da kuma saurin dorawa 8.77 Mbps.
Ku yi "like" "comment" ko "share" don sauran abokai su amfana.

Muna maraba da shawarwari, karin bayani ko tambayoyin da suka shafi Maudu'i.

Ku ziyarce mu a dandalin sada zumunta a Facebook Duniyar Yana don samun Mukaloli da dumi dumin su.

Comments

Post a Comment

Muna maraba da karin bayani ko sharhi

Popular posts from this blog

GARABASA

HASASHEN KIMIYYA 8 DA SUKA FARU A ZAHIRI