Posts

Showing posts from July 15, 2018

GARABASA

Image
GARABASA Shahararren kamfanin sadarwa na  Airtel Nigeria  ya sake zuwa da wata sabuwar garabasa a bangaren data. Da kudi kalilan zaka sayi data mai dimbin yawa ta yadda zaka samu daman shiga yanar gizo, ka sauke abubuwa masu yawa da kudi kadan. A yanzu dai kamfanin ta ribanya adadin datar da take bayarwa har sau biyu ba tare da ta kara sisin kwabo ba. Wannan ba karamin ci gaba bane musamman ga 'yan makarantar da waɗan da basu da mahaɗar Wi-Fi da masu karamin karfi idan aka yi d uba da yadda al'amuran yau da kullum suke ta komawa yanar gizo. Ga jerin lambbobin sayan datar a kasa: 1.5GB akan ₦500 danna *418# 3GB akan ₦1000 danna *496# Idan kana son sayen datar sama da haka, danna *141# sai ka canki zabin ka. Abin lura: Wannan garabasa tana aiki ne akan sabon layin Airtel. Idan baka da shi kayi maza ka garzaya shagon Airtel mafi kusa da kai saboda kada ayi ba kai. Masu tsofin layin Airtel zasu danna *144# don duba cancanta. Muna maraba da karin ba