Posts

ABUBUWA 12 DA BAI KAMATA KA WALLAFA A FACEBOOK BA.

Ko da kana tunanin ka saita “Privacy” baka da tabbacin iyakar masu ganin bayanan da kake rubutawa. Baka da ikon kayyade abinda abonkanan ka zasu iya yi da bayanan da kake wallafawa. Kada kayi la’akari da karancin “comments” ko “likes” saboda masu karanta rubutunka suyi gaba sun fi yawa ba tare da ka sani ba. Kenan abu ne mai sauki post dinka ya bayyana a inda baka tsammani musamman idan aka yi “searching”. Ga wasu abubuwa guda goma sha biyu masu muhimmanci da ya kamata ka killace daga Facebook. 1.Bayanai game da kai na hakika wadannan suka shafi sirrinka na zati. Kada ka rubuta abinda ka san ya dace da bayananka na banki irin su; adireshin gida, sunan mahaifiya, lambar waya, kwanan watan haihuwa da dukkan dangogin su. Irin wadannan bayanai ne masu “satar zati” (identity-teft) suke sacewa suna aikata ta’adancin yanar gizo (cyber crime). Saboda haka maganin da banyi ba shine ban fara ba. 2.Kalmomin sirrin ko ta kwana “password hints” da “security questions.”

YI KIRA KYAUTA TARE DA CUG SIM CARD

Image
YI KIRA KYAUTA TARE DA CUG SIM CARD. Matashiya; Kaman yadda muka yi alƙawari a baya cewa post na gaba zai yi bayani akan layin POL COM ko CUG, to gashi Allah Ya nufa. A baya mun yi bayani game da SPECIAL NUMBER da alfanun sa, yanzu kuma zamu yi bayani akan CUG SIM wanda ake yin kira kyauta dashi. MENE NE POL COM ko CUG? CUG (Closed User Group) layi ne wanda kamfani take bugawa don jami'an tsaro ko hukumomin gwamnati don saukaka masu wajen yin kira ba tare da sisin kwabo ba. A da can kamfanin GLO NG ne kadai suke buga irin wadannan nau'ikan layika, amma yanzu sauki yazo saboda shahararren kamfanin Airtel Nigeria yayi hobbasa ya fitar da CUG SIM CARD don saukakawa dukkan yan kasa. ALFANUN CUG SIM CARD. 1. Kira kyauta daga CUG zuwa CUG. 2. x10 bonus a kowane lodin da aka yi. Bonus ɗin yana rabuwa kashi kashi kaman haka; a) Bangaren kiran kowane network, b) Bangaren kiran Airtel zuwa Airtel, c) Bangaren kiran Family And Friends (FAF) ma'ana yan uwa da abokan

SPECIAL NUMBER DA ALFANUN TA

Image
ALBISHIR DIN KU KANAWA!!! Ga wata dama tana zuwa da ba kasafai ake samun irin ta ba. Shin ko ka taba mallaka ko jin labarin layin waya da ake yiwa lakabi da suna SPECIAL NUMBER? Ka taba mallaka jin labarin wasu layikan waya POL COM da CUG? Shahararren kamfanin na wato Airtel Nigeria ya zo maku amsoshin tambayoyin dake sama. MENE NE SPECIAL NUMBER? Special number layi ne na musamman da ba kasafai ake samun irin sa ba, layi ne da kamfani take bugawa domin saukakawa kwastomomi wajen haddace lambobi. ALFANUN SPECIAL NUMBER 1. Manyan mutane, yan kasuwa, gidajen Radiyo da na Talabijin suna amfani da special numbers don saukaka mu'amala ga abokan hulɗar su. 2. Special number yana da kwarjini da burge mutane a duk lokacin da ake karanta shi. 3. Yana zuwa da wasu damammaki da ba a cika samu a layika gama gari ba. 4. Yana zuwa da fasaha mafi ƙarfi wato wajen kira da saurin shiga yanar gizo wato 4G LTE. 5. Yana zuwa da "double data offer" ma'ana za&

GARABASA

Image
GARABASA Shahararren kamfanin sadarwa na  Airtel Nigeria  ya sake zuwa da wata sabuwar garabasa a bangaren data. Da kudi kalilan zaka sayi data mai dimbin yawa ta yadda zaka samu daman shiga yanar gizo, ka sauke abubuwa masu yawa da kudi kadan. A yanzu dai kamfanin ta ribanya adadin datar da take bayarwa har sau biyu ba tare da ta kara sisin kwabo ba. Wannan ba karamin ci gaba bane musamman ga 'yan makarantar da waɗan da basu da mahaɗar Wi-Fi da masu karamin karfi idan aka yi d uba da yadda al'amuran yau da kullum suke ta komawa yanar gizo. Ga jerin lambbobin sayan datar a kasa: 1.5GB akan ₦500 danna *418# 3GB akan ₦1000 danna *496# Idan kana son sayen datar sama da haka, danna *141# sai ka canki zabin ka. Abin lura: Wannan garabasa tana aiki ne akan sabon layin Airtel. Idan baka da shi kayi maza ka garzaya shagon Airtel mafi kusa da kai saboda kada ayi ba kai. Masu tsofin layin Airtel zasu danna *144# don duba cancanta. Muna maraba da karin ba

MENE NE 4G LTE?

Image
4G LTE Kana son shiga cikin masu more tsarin fasahar internet mafi sauri a wayar ka? Yi maza ka koma kan fasahar 4G LTE . MENE NE 4G LTE? Fourth Generation Long Term Evolution , wanda aka fi sani da 4G LTE shine fasaha mafi sauri wajen gudanar da ayyukan yanar gizo a Nigeria, yana samun karbuwa wajen masu amfani da manyan wayayoyi masu dauke da manhajar komi da ruwanka wato Android , da Mi-Fi ko Router da kuma Modem . 4G LTE fasaha ce mai saurin gaske wadda take bada damar gudanar da ayyuka masu nauyi cikin kyaftawar ido. Zaka iya yin kira mai hoto rangadadau wata " HDvideo call " ba tare da wani jinkiri ba. Zaka iya sauko da lodi mai nauyi cikin kankanin lokaci. Da 4G LTE , zaka iya kallon tafsir kai tsaye ta cikin youtube ko facebook go live, ko live on instagram. KAMFANONIN DA SUKE DA FASAHAR 4G LTE A NIGERIA. 9mobile (Etisalat) a da, Globacom, MTN, NTEL, Spectranet, Swift, Smile, Airtel. Za mu dau misalin yadda ake shiga tsarin fasaha